Dauda Kahutu Rarara - Aisha (Official Music Video)

Dauda Kahutu Rarara
Dauda Kahutu Rarara
0 بار بازدید - 4 هفته پیش - ✍️  Ki bar mana kuka
✍️  
Ki bar mana kuka (Aisha)
A'i ki bar mana kuka (Aisha)
Da baya, da baya (Aisha)
In dan tuna baya (Aisha)
Rawar fasa kwarya (Aisha)
Ba a raba ni dake zinariya
Ki bar mashi kuka (Aisha)
Baki da tamka (Aisha)
Bai iya komai, in ba tare da ke ba Aisha
Ki bar mani kuka (Aisha)
Baki da tamka (Aisha)
Bazan iya komai, in ba tare da ke ba Aisha
Aisha
Aisha
Da kunu da kunama, bance maku gara kunu ba (Aisha)
Da Bala da bala'i, bance maku gara Bala ba (Aisha)
Da fate da fatanya, bance maku gara fate ba (Aisha)
Da are da aradu, ba lallai gara are ba (Aisha)
Dan wasu ban yi dasu ba (Aisha)
Baiwa ya hishi samu (Aisha)
Abun wasu gara abun mu (Aisha)
Na'ima taga Tanimu dan Abdul aka nemo zabiya
Aisha
Masu san katarar giwa ku gaya masu ta masu nauyi (Aisha)
Dumi a saman murhu ku cire masa ya masa nauyi (Aisha)
Ruwan da kwan randa ko da ban sha ba da sanyi (Aisha)
Kyankyasa ko kun san ba'a sai basuda boyi (Aisha)
Ko ga kura tandu (Aisha)
Kwalli sai da masayi (Aisha)
'Da ya wuce bayi (Aisha)
Gauro sai da majanyi (Aisha)
Ku ji in haka yayi Indo ce mai daka ni kuma Aisha
Aisha ita komai nata daban yake
Za kaga ko da ma wankanta daban yake
Aza kallabi, daurin dan kwalinta daban yake
Kuga sarkoki, har ma dan kunnenta daban yake
Hatta ladabi da biyayya tata daban yake
Indo dada ke nake
Makiya dada sun sake
Dan kin barsu a tsallake
Aisha, Indo Aisha turmi sha daka
Indo A'i fadi take a cikin biyu
Ke nace, "Muyi mu biyu"
Ashe kina da hali biyu
Su A'i masu gida biyu
Jira nake kiyi 'yan biyu
Ayya kai, gashi Jamila tayi bari
Ranar jajibari
Wai dan tsun-tsu ya ga kwari
Yace, "A harbo yayi uzuri"
Gyada sarkin sukari
In mutu zaki sai sikari
A'a haske raya gari
Tantabara 'yar alkawari
Ga goron albishiri zaku ji in kum bani gari
Ari-riya-ri-riya (Aisha)
Da 'yar sarkar wuya (Aisha)
Da gani ba tambaya (Aisha)
Ga matata nan warda ta ke mani wanka (Aisha)
Na isheta turaka (Aisha)
Na saka mata kuka
Wai-wai-wai-wai-Aisha
Wai-wai-wai-wai-Aisha
Aisha, Indo Aisha na sara maki
Aisha, Indo Aisha turmi sha daka
Gimbiya, mata sun bida, sun kyale mu
Aisha, Indo Aisha turmi sha daka
Sarauniya, mata sun riga sun kyale miki
Aisha, Indo Aisha turmi sha daka
Uwar gida, gani gabanki, har na duka maki
Aisha, Indo Aisha turmi sha daka
Dan sai da ke, dan kuwa na riga na yarje miki
Aisha, Indo Aisha turmi sha daka
Ga garkuwa, maza take sanar dani komai zan miki
Aisha, Indo Aisha turmi sha daka
Aisha, Aisha (turmi sha daka)
Aisha, Aisha
A cikin biyu Aisha (Turmi sha daka)
Aisha, Indo Aisha
Aisha, a cikin biyu Aisha
4 هفته پیش در تاریخ 1403/03/17 منتشر شده است.
0 بـار بازدید شده
... بیشتر